Majalisar Dokoki jiya ta yi watsi da kudurin lokutan zabe wanda shugaba Muhammadu Buhari ya ki amincewa da shi.
Zaurukan majalisar biyu jiya ba su kula da sabon kudurin ba biyo bayan kin amincewar da shugaban kasar ya yi da gyaran da suka yi wa dokar zaben ta shekarar 2010.
Shugaba Buhari ya ki amincewa da gyaran fuskar da majalisar ta yi inda ya kafa hujja da dokokin Najeriya.
A majalisar, ’yan majalisar sun yanke shawarar su janye tattauna batun sabuwar dokar wacce ake yi mata taken “Kudurin dokar da zai yi gyaran fuskar dokar zabe don bayar da damar yi wa lokutan zaben gyaran fuskar wanda Sanata Sulaiman Nazifi dan jama’iyyar APC daga jihar Bauchi ya dauki nauyi.