Majalisar Dattawa ta yi watsi da kudurin da ke neman Gwamnatin Tarayya ta sake bude iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Da yake gabatar da kudurin a ranar Talata, Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya bayyana wa majalisar cewa rufe iyakar ya haifar da wahalar rayuwa musamman ga a’ummomin yankunan da ke iyaka da Nijar a jihohin Sakkwato, Kebbi, Zamfara, Katsina, Jigawa, Yobe da Borno.
Sanata Kawu Sumaila ya kuma kara da cwea rufe iyakar ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya na tabbatar da tsaro da kuma walwalar jama’a.
Don haka ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta sake bude iyakokin domin a samu shige da ficen kayayyaki a tsakanin kasashen biyu.
Amma Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya ce majalisar ta riga ta cimma matsaya tafiya da matakin da kungiyar ECOWAS ta dauka kan rikicin na Nijar.
ECOWAS ta dauki matakan da suka hada da hana shawagin jirgi a Nijar da kuma rufe iyakokinta da kasashen kungiyar da ma yiwuwar daukar matakin soji domin matsa wa sojojin su mika mulki.
Akpabio ya ce akwai bukatar Majalisar ta samu cikakken bayana daga sojoji kan halin da ake ciki kan lamarin na Nijar, kafin a nemi bude iyakokin.
Saboda haka ya bukaci Sanata Kawu ya janye kudurin, wanda nan take ya bi umarnin.
A watan Agusta Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin rufe iyakar Najeriya da Nijar, domin matsa wa sojojin da suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum su koma bariki su dawo wa shugaban kan kuerersa.