✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe ’yar dan Majalisar Borno a gidan mijinta

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun yi wa ’yar dan majalisar dokokin Jihar Borno mai wakiltar Ngala, Bukar Abacha, kisan…

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun yi wa ’yar dan majalisar dokokin Jihar Borno mai wakiltar Ngala, Bukar Abacha, kisan gilla a gidan mijinta.

Aminiya ta gano an kashe ta ne ta shake ta har lahira a kusa da Gidan Dembe da ke garin Maiduguri, a ranar 17 ga Oktoba, 2023.

Bayanai sun nuna cewa mijinta ne ya ya kai gawarta ofishin ’yan sanda, inda ya shaida musu cewa  ya tarar da gawarta a gidansa adaure da hannunta da kafafunta a bayanta, yaronta dan shekara biyu yana gefe yana kuka.

Rundunar ’yan sanda ta Gwange da ke Maiduguri ta kwashi gawar marigayiyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri domin gudanar da bincike.

Faruwar wannan lamarin dai ya haifar da tashin hankali ga al’umma inda suke ta yin tururuwa zuwa wajen don gane wa idonsu abin da ke faruwa.

Rundunar ’yan sandan ta lashi takobin zakulo wadanda ke da hannu a kisan gillar don gurfanar da su gaban kuliya.