Majalisar Dattawa ta yi watsi da bukatar Shugaba Buhari na soke sashen da ya haramta wa ministoci da masu rike da mukaman siyasa tsayawa takara ko zaben ’yan takarar siyasa.
A zaman Majalisar ta ranar Laraba, Sanatocin sun yi ittifaki wajen yin fatali da bukatar Buhari na soke Sashe na 84 (12) na Dokar Zabe ta 2022 da Buharin ya sanya wa hannu a kwanakin baya.
- Shugaban Kwamitin Binciken Abba Kyari ya rasu
- Kotu ta ce ba wanda ya tursasa Abdulmalik Tanko ya ce shi ya kashe Hanifa
Tun kafin jefa kuri’ar fatali da bukatar ta sauya bangaren dokar, ’yan Majalsiar da suka yi tsokaci sun bukaci a jingine batun saboda kotu ta ba da umarnin hana majalisar daba dokar.
Sai dai kuma da yake martani, Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana cewa kotu ba ta da hurumin hana Majalisa yin aikinta na yin dokoki ko yi musu gyaran fuska ba.