✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta yi wa kudirin soke bautar kasa karatun farko

Kudirin dokar ya tsallake karatun farko a zauren Majalisar Wakilai.

Kudirin dokar neman a soke yi wa kasa hidima ya tsallake karatu na farko a zauren Majalisar Wakilan Najeriya.

Dan Majalisa Awali Inombek Abiante na jam’iyyar PDP daga Jihar Ribas ne ya gabatar da kudirin yayin zaman majalisar na ranar Litinin.

Abiante ya bayyana dalilai na bukatar rushe Hukumar Masu Yi wa Kasa Hidima (NYSC) da suka hada da matsalar tsaro da kasar ke fuskanta da kuma badakalar da ta dabaibaye yadda ake tura masu yi wa kasar hidima wuraren da za su kama aiki.

Kudirin dokar na neman a yi wa sashe na 315 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 kwaskwarima, wanda ya kunshi tanade-tanaden da suka shar’anta yi wa kasar hidima.

A cewar Abiante, ci gaba da kashe-kashen ’yan hidimar kasa a sassa daban-daban na Najeriya nan da ’yan bindiga da ’yan ta’adda ke yi, ga rikicin kabilanci da na addini, wanda duk suna barazana ga rayukan dubban masu yi wa kasa hidima.

Babu shakka matsalar tsaro ta zama ruwan dare a fadin Najeriya, wanda a sanadiyyar haka rayukan dubban mutane sun salwanta.

Alkaluma na tarihi sun ce, a ranar 22 ga watan Mayun 1973 aka kirkiri Hukumar NYSC, a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon.

An kirkiri hukumar ce bayan yakin Basasa a wani yunkuri na shimfida dabarun da za su tabbatar da hadin kai a kasar.