Majalisar Wakilai ta yi fatali da bukatar Shugaban Kasa Bola Tinubu ta kashe Naira biliyan 5 daga cikin kwarya-kwaryar kasafin kudin tiriliyan 2.17 wajen sayen jirgin ruwa.
A maimakon haka, majalisar ta bukaci a kara kudin a bisa wanda aka ware domin ba dalibai rance, wanda a baya aka ware wa biliyan 10.
- ‘Barayin’ da suka je fashi sun ɓige da satar tukwanen miya da abinci a Kalaba
- Majalisa ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kudin Tinubu na tiriliyan 2.17
Aminiya ta rawaito cewa matakin ’yan majalisar ba zai rasa nasaba da koke-koken da ’yan Najeriya suka rika yi ba tun bayan bullar labarin sayen jirgin ruwan shugaban kasar, a daidai lokacin da suke cikin kuncin rayuwa.
Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Abubakar Kabir (APC, Kano) ne ya bayyana hakan lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi jim kadan da kammala amincewa da kasafin a Abuja.
Ya ce daukar matakin ya zama wajibi la’akari da kudin da aka ware wa daliban a cikin kasafin ya yi kadan.
Abubakar ya kuma ce kwamitin ya kara kason da aka ware wa Ma’aikatar Tsaro daga Naira biliyan 476 zuwa 546 sakamakon ƙaruwar kalubalen tsaro.
Shugaban kwamitin ya kuma ce sun duba tare da amincewa da batun kara mafi ƙarancin albashin ma’aikata domin mika shi ga bangaren zartarwa.
Ya ce za su tabbatar suna sanya idanu ga bangaren zartarwa domin ganin an yi abin da ya dace.
Amma daga bisani Fadar Shugaban Kasa ta ce jirgin ruwa ba na amfanin Tinubu ba ne, na Rundunar Sojin Ruwan Najeriya ne.