Majalisar Dattawa ta yi amfani da rahoton da DailyTrust/Aminiya ta buga kan yadda aka kara kudin kwangilar dakin karatu na kasa daga Naira biliyan takwas da digo biyar zuwa naira biliyan 38 da digo bakwai a cikin shekara 10.
A watan Oktoban shekarar 2016 jaridar Aminiya ta buga wani labari na musamman kan yadda aka bayar da kwangilar a shekarar 2016 ga kamfanin gine-gine na Messrs Reynolds a kan kudi Naira biliyan takwas da digo 590 wanda ake sa ran a kammala a watanni 22 amma kuma aka kara kudin kwangilar zuwa biliyan 38 da digo bakwai.