Majalisar Dattawa ta tantance Festus Keyamo daga Jihar Delta a matsayin minista bayan dambarwar da ta mamaye tantacewar farko.
Festus Keyamo ya bayar da hakuri a kan kuskurensa na baya, inda ya ki amsa gayyatar majalisa ta 9 kan ayyukansa a matsayin Karamin Ministan Kwadago.
- An rantsar da mace a matsayin alkaliyar alkalan Kano
- An rantsar da mace a matsayin alkaliyar alkalan Kano
A lokacin zaman tantancewar, Sanata Darlington Nwokocha daga Jihar Abiya ya fargar da majalisar a kan yadda a baya Keyamo ya nuna “rashin da’a” ga majalisa ta 9, inda ya zargi majalisar da aikata rashawa.
Tsohon Ministan Kwadagon ya bayar da hakuri sannan ya yi karin haske kan abubuwan da suka faru a wancan lokacin.
Da farko dai Sanata Darlington ya nemi a dakatar da tantance Keyamo, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce har ya kai ga tsaiko ga aikin tantancewar.
Daga baya dai majalisar ta dawo ta kuma yafe masa laifin da ya yi a baya.
Festus Keyamo ne mutum na karshe da majalisar ta tantance daga cikin 48 da Shugaba Bola Tinubu ya aike mata don amincewa da su a matsayin ministoci.
Festus Keyamo shi ne ministan gwamnatin Buhari da ya sake shiga cikin jerin sunayen wadanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai nada a matsayin minista
Kawo yanzu bayan shafe kwanaki takwas ana aikin majalisar ta tantance mutum 45 kamar yadda Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio ya sanar.
Ragowar ukun da majalisar ta tantance amma ake jiran a tabbatar da su ta fuskar tsaro sun hada da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai da Abubakar Sani Danladi daga Jihar Taraba da kuma Stella Okotete daga Jihar Delta.
Wadanda aka kammala tantacewa sun hada da:
Akwa Ibom: Ekperikpe Ekpo
Bayelsa: Heineken Lolokpobri
Kuros Riba: Betta Edu
Kuros Riba: John Enoh
Edo: Abubakar Momoh
Ribas: Nyesom Wike
Adamawa: Tahir Mamman
Bauchi: Yusuf Maitama Tuggar
Bauchi: Ali Pate
Borno: Abubakar Kyari
Gombe: Alkali Ahmed Saidu
Taraba: Uba Maigari Ahmadu
Yobe: Ibrahim Geidam
Jigawa: Mohamed Badaru
Kano: Mariya Mahmoud Bunkure
Kano: Abdullahi T. Gwarzo
Katsina: Ahmad Dangiwa
Katsina: Hannatu Musawa
Kebbi: Yusuf Tanko Sununu
Kebbi: Atiku Bagudu
Sakkwato: Bello M. Goronyo
Zamfara: Bello Matawalle
Abia: Nkiruka Onyejiocha
Anambra: Uju Ohaneye
Ebonyi: David Umahi
Enugu: Uche Nnaji
Imo: Doris Uzoka
Ekiti: Dele Alake
Legas: Tunji Alausa
Legas: Lola Ade-John
Ogun: Isiak Salako
Ogun: Bosun Tijjani
Ogun: Olawale Edun
Ondo: Olubunmi Tunji-Ojo
Osun: Adegboyega Oyetola
Oyo: Adebayo Adelabu
Benuwe: Joseph Utsev
Abuja: Zaphaniah Bitrus Jisalo
Kogi: Shuaibu A. Audu
Kwara: Lateef Fagbemi
Nasarawa: Imaan S. Ibrahim
Neja: Mohammed Idris
Neja: Aliyu Sabi Abdullahi
Filato: Simon Lalong
Delta: Festus Keyamo