A ranar Talata Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Farfesa Mahmud Yakubu a matsayin Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a karo na biyu.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya sake nada shi bayan wa’adinsa na farko da ya fara tun shekarar 2015 ya cika a watan Oktoban 2020.
- Shugaban INEC ya sauka daga mukaminsa
- INEC ta dage zaben cike gurbi zuwa 5 ga Disamba
- INEC na shirin fara zabe ta intanet a 2021
- Kasafin 2021: INEC ta bayyana a gaban Majalisa
Tabbatarwar ta biyo bayan nazarin rahoton da Kwamitin Majalisar Dattijai kan INEC, karkashin jagorancin Sanata Kabiru Gaya ya gabatar a zaurenta.
Yayin gabatar da rahoton, Sanata Gaya ya ce Ykubun ya cancanci sake shugabancin hukumar ta INEC don haka suka ba da shawarar a tabbatar da shi.
Sanatocin jam’iyyar adawa wadanda suka yi magana bayan gabatar da rahoton sun goyi bayan nadin Yakubu, suna masu cewa ba ya nuna son kai a ko fifikon siyasa a aikinsa.
Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, Sanata Enyinnaya Abaribe ya yaba wa Yakubu kan sabbin fasahohin da ya kirkiro a hukumar ta INEC, musamman yadda sakamakon zabe ke zuwa babbar tashar tattara sakamako daga rumfunan zabe.
Ya ce yana tafiya kan turbar da ta dace kuma ya kamata su ba shi goyon bayan da ya dace, in ji Sanata Sandy Onor dan PDP daga jihar Kuros Riba.
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya taya wanda aka zaba murna tare da yi masa fatan samun nasara a karo na biyu.