Majalisar Dattawa ta sahale wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta rika aika sakamakon zabe ta intanet.
Hakan na zuwa ne bayan matsin lamba na tsawon watanni da majalisar ta fuskanta a kan sauya ra’ayinta na farko da ta hau kujerar naki a kai.
- ’Yan sanda sun ceto uwa da ’yarta daga hannun masu garkuwa
- Mutum 7 sun rasu, 12 sun ji rauni a hatsarin mota
A zamanta na ranar Talata, majalisar ta sauka daga ra’ayinta na farko wanda ta ki amincewa da matakin da zai bai wa INEC lasisin tura sakamakon zabe kai tsaye daga mazabu ta hanyar yanar gizo.
Tun a watan Yulin da ya gabata ne Majalisar Dattawan yayin amincewa da kudirin yi wa dokar zabe kwasakwarima, akwai tanadin da aka yi wa INEC na amfani da na’ura wajen aika sakamakon zabe idan har Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta NCC ta amince.
Kudirin kamar yadda Majalisar Wakilai ta zartar, ya bai wa INEC damar tura sakamakon zabe kai tsaye ta Intanet a duk sa’ilin da bukatar hakan ta taso.
Rahotanni sun ce majalisar ta kuma amince da tsarin gudanar da zaben fidda ’yan takara na jam’iyyu ta hanyar zabe kai tsaye tare da sa idon hukumar INEC.