✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta kori minista kan daukar ma’aikata 774,000

Cacar baki kan shirin daukar ma’aikata 774 ,000 aiki na hukumar ayyuka ta NDE ta sa Majalisar Dattakawa korar Karamin Ministan Kwadago da Ingantuwar Aiki…

Cacar baki kan shirin daukar ma’aikata 774 ,000 aiki na hukumar ayyuka ta NDE ta sa Majalisar Dattakawa korar Karamin Ministan Kwadago da Ingantuwar Aiki Festus Keyamo.

Gwamantin Tarayyar ta yi shirin na SPP ne wanda za a fara a watan Oktoba, da zummar daukar matasa 1,000 daga dukkan Kananan Hukumomin Najeriya 774, da za su yi kananan ayyukan wuci gadi a kan albashin Naira 20,000.

Majalisar ta gayyaci Keyamo da jami’an NDE, wadda ita ce aikin ke hannunta, domin bin bahasi kan shirin daukar aikin wanda a kansa ne NDE ta kafa kwamitin mutum 20-20 na masu daukar aikin a kowace jiha.

Liki ya fara tashi ne sadda ‘yan majalisar suka yi zargin rashin daidaito a zabar ‘yan kwamitocin, wadanda shugaban NDE Nasiru Ladan ce mutum takwas-takwas daga cikinsu kadai ya san yadda aka zabo su.

Hayaniya ta kaure ne bayan ‘yan majalisar sun bukaci Keyamo ya yi bayani kan bambacin da aka samu a cikin sirri, amma ya ce atafau, sai dai a yi komai a gaban ‘yan jarida don su san yadda aka zabo ‘yan kwamitocin.

Jijiyoyin wuya sun kara tashi ne bayan ‘yan majalisar sun zargi ministan da neman zabar yadda zaman da suka kira zai gunana.

Bayan cacar bankin ne ‘yan majalisar suka bukaci ya ba su hakuri. “Idan ba zai ba da hakuri ba ya tattara ya yi gaba,” inji wani dan majalisar.

Amma ministan ya kekashe kasa cewa shi bai bai fada musu wata yasasshiyar magana ba.

Su kuma daga nan suka ce masa ya tafi ya ba su wuri.