Majalisar Dattawa ta ki amincewa da hadimar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a dandalan sada zumunta, Lauretta Onochie a matsayin Kwamishina a Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).
Hakan na zuwa ne yayin da Majalisar ta karbi rahoton Kwamitin INEC, wanda Sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Gaya na jam’iyyar APC ke jagoranta.
- Mulkin ’yan uwa da abokai ake yi a Gombe ba siyasa ba — Dan Barde
- Miji ya gano bidiyon auren matarsa da wani
Kwamitin da Sanata Gaya ke jagoranta ya ce nadin Onochie a matsayin Kwamishina ta Hukumar INEC ya ci karo da sashe na 14 cikin kundin tsarin mulkin kasa na 1999 da aka tanadar a cikin tsare-tsaren Hukumar Tabbatar da Raba Daidai na Ma’aikata.
Majalisar ta ce akwai wata ’yar Jihar Delta, May Agbamuche-Mbu, inda Lauretta ta fito da ita ma Kwamishina ce a Hukumar, don haka ba za a iya bai wa mutum biyu daga jiha guda ba.
A yau Talata ce Majalisar ta gudanar da zaman tantance mutum bakwai da Shugaban Kasar ya aike da sunayanensu don nada su Kwamishinoni a INEC.
Sauran wadanda Majalisar ta amince akwai Farfesa Sani Kallah, Farfesa Kunle Cornelius Ajayi, Farfesa Sa’idu Babura Ahmad, Dokta Baba Bila da Farfesa Abdullahi Zuru.
Majalisar ta kuma jingine amincewa da Farfesa Sani Mohammed Adamu, har sai hukuncin da za ta yanke a nan gaba.
A kan haka ne Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan, ya umarci kwamitin da ya sake fadada bincike sannan ya dawo da rahoto nan da mako biyu masu zuwa.