✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta kammala karatu na biyu a kan kasafin 2021

Majalisar ta gama karatu na biyu a kan kasafin mako guda bayan Buhari ya mika mata

Majalisar Dattawa ta kammala karatu na biyu a kan daftarin kasafin 2021.

Kamalla karatu na biyun na zuwa ne mako guda bayan Shuaba Buhari ya gabatar wa Majalisar Tarayya kasafin na Naira tiriliyan 13.08.

Majalisar Dattawa ta yi kwana uku tana muhawara a kan daftarin kafin ta kammala karatu na biyu a kansa.

Daga nan Shugabanta, Sanata Ahmad Lawan ya tura kasafin ga Kwamitin Kasafi na Majalisar domin ci gabda da aiki.

Ahmad Lawan ya bukaci kwamitin wanda Sanata Barau Jibrin ke jagoranta da ya kawo wa rahoto cikin mako hudu.