Majalisar Dattawa ta gindaya sharudan da za a bi kafin a iya kirkirar sabbin jihohi a Najeriya.
Kwamitin yi wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 Kwaskwarima na Majalisar ya karbi gwamman bukatun kirkirar sabbin jihohi daga sassa daban-daban na kasar yayin tarukan jin ra’ayin jama’a a kwanakin baya.
Sai dai Majalisar Dattijan ta ce dole kowace bukatar kirkirar sabuwar jiha ta dace da tanade-tanaden sashe na takwas na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima.
Mai magana da yawun Majalisar, Sanata Ajibola Basiru ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi.
Sanarwar ta kuma karyata labarin da ya karade gari cewa rahoton kwamitin ya ba da shawarar kirkiro sabbin jihohi guda 20.
Ya ce daga cikin abin da Kundin Tsarin Mulkin ya tanada akwai gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a ga akalla kaso biyu bisa uku na mutanen yankin, da kuma samun amincewar kaso biyu bisa uku na dukkan mambobi Majalisun Tarayyar guda biyu.
Ya ce, “Labarin da aka yada ko kusa bai yi da abin da rahoton kwamitin ya kunsa ba game da kirkiro sabbin jihoh.”
“Ya zama dole mu yi bayani domin warware zarce da bawa,” inji shi.
Ya ce duk da bukatar kirkirar sabbin jihohin da aka gabatar, ba hurumin kwamitin Majalisar Dattawan ba ne yin hakan, saboda haka ya mika lamarin ga hukumar zabe ta kasa (INEC) domin cika sharuddan sashe na takwas na Kundin Tsarin Mulki da ya tanadi a gudanar da zaben raba gardama idan har kudirin ya samu amincewar kashi biyu cikin uku na ’yan Majalisar Wakilai, Majalisar Dattawa da kuma Majalisa Jiha daga yankin da abin ya shafa.