✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta gargaɗi MTN kan yawan ɗaukewar sabis a Katsina

Kamfanin ba shi ba da wani uzuri ko cikakken bayani kan dalilin ɗaukewar sabis ɗin.

Majalisar Dokokin Katsina ta gargaɗi kamfanin sadarwa na MTN dangane da yawan ɗaukewar sabis ba tare da yi wa al’umma wani gamsasshen bayani ba.

BBC ya ruwaito majalisar na bayyana takaicinda cewa yawan ɗaukewar sadarwar na cutar da kasuwanci da zamantakewar al’ummar jihar.

Cikin wani ƙudirin gaggawa da ɗan majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Dandume, Honarabul Yahaya Nuhu Mahuta ya gabatar a zauren Majalisar ranar Talata, ya ce katse sabis da kamfanin ke yi ya shafi ɓangarorin kasuwanci, ilimi da harkokin yau-da-kullum.

Mataimakin Kakakin Majalisar, Honarabul Abduljalal Haruna Runka ya shaida wa BBC cewa haƙƙin kamfanin ne ya samar da nagartattun ayyuka, domin al’umma kuɗi suka biya don neman biyan buƙata.

Ya bayyana cewa babban takaicin, kamfanin ba shi ba da wani uzuri ko cikakken bayani kan dalilin ɗaukewar sabis ɗin.

Honarabul Mahuta ya ce al’umma suna da haƙƙin a kan kamfanin, kuma gazawar zai bai wa al’ummar damar canza tsarin da suke ganin zai taimake su.

Haka kuma, majalisar na duba yiwuwar gayyato kamfanin domin ya gabatar da gamsasshen bayani ga majalisar kan dalilin ɗaukewar sabis ɗin.

Mataimakin kakakin majalisar, ya umarci kwamitin sadarwa na majalisar ya aiwatar da bincike a kan koken, tare da kawo rahoto nan da mako biyu.