✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta dakatar da daukar ma’aikata 774,000

Majalisar Tarayya ta dakatar da Gwamnatin Tarayya daga daukar ma’aikata 774,000  har sai an yi  mata cikakken bayani. Majisar Dattawa da ta Wakilai sun bukaci…

Majalisar Tarayya ta dakatar da Gwamnatin Tarayya daga daukar ma’aikata 774,000  har sai an yi  mata cikakken bayani.

Majisar Dattawa da ta Wakilai sun bukaci Ministan Kwadago Chris Ngige da jami’ansa zo su yi musu bayanin yadda za a aiwatar da shirin daukar ma’aikatan, bayan cacar baki da kwamitin majalisar dattawa ya yi da Karamin Ministan Kwadago Festus Keyamo a kai.

“Dole a yi mana bayani da zai gamsar da jama’a kan yadda za a aiwatar da shirin yadda ya kamata, a matsyinmu na wakilan al’umma wadanda da mu aka tsara shirin aka amincewa da shi da kuma ware masa kudade”, inji sanarwar hadin gwiwar majalisun na ranar Laraba.

Shirin na daukar kananan ma’aikatan wucin gadi 1,000 daga kowacce daga kananan hukumomin Najeriya 774 na daga cikin matakan da gwamnati ta fitar a domin rage wa ‘yan kasa masu karamin karfi radadin cutar coronavirus.

Rikicin na ranar Talata ya kunno kai ne bayan ‘yan kwamitin majalisar sun yi zargin rashin daidaito a zabin mutum ashirin-ashirin ‘yan kwamitin daukar aikin a jihohi.

Bayan Keyamo da shugaban kumar NDE mai kula da shirin, Nasiru Ladan, sun sha bamban kan zadda aka zabo wasu daga cikin ‘yan kwamitin jihohin ne kwamitin majalisar ya bukaci a yi masa bayani cikin sirri domin samun daidaito kan bambancin.

Amma Keyamo ya ce sai dai a yi komai a gaban ‘yan jarida, har ta kai ga fadi-in-fada tsakaninsa da ‘yan kwamitin majalisar da suka ce yana neman juya su.

‘Yan kwamitin sun nemi ya ba su hakuri amma ya ce ba zai yi ba saboda shi bai aikata ba daidai ba, su kuma suka ce ya tafi ya ba su wuri.