Majalisar Dattawa, ta buƙaci Ma’aikatar Sadarwa da ta yi aiki tare da kamfanonin sadarwa domin rage kuɗin data, ta yadda kowa zai iya samun Intanet mai sauƙi a Najeriya.
A zaman majalisar na ranar Laraba, Sanata Asuquo Ekpenyong (APC – Kuros Riba), ya nuna damuwa kan yadda farashin data ya ƙaru da kusan kashi 200.
- Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago
- Kakakin ’yan sandan Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu
Ya ce ƙarin yana hana mutane da dama musamman matasa, samun damar amfani da Intanet.
“Ƙarin farashin data ba wai kawai yana hana mutane shiga Intanet ba ne, har ma yana wahalar da matasa ’yan kasuwa da masu aiki daga gida,” in ji Sanata Ekpenyong.
Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya jaddada cewa samun Intanet mai arha zai taimaka wa ƙananan ’yan kasuwa da tattalin arziƙin ƙasa gaba ɗaya.
Majalisar ta buƙaci gwamnati da ta tsara manufofi da za su tabbatar da farashi mai sauƙi, tare da kafa cibiyoyin fasaha masu rangwame ga ɗalibai, ’yan kasuwa, da masu aiki da fasahar zamani.
Haka kuma, ta umarci Kwamitin Sadarwa na majalisa da ya binciki dalilan tashin farashin data tare da nemo mafita mai ɗorewa.