Majalisar Dokoki ta bukaci dakarun sojin Najeriya da su yi amfani da kayan yakin da gwamnati ta samar wajen kawo karshen hare-haren ’yan bindiga a Arewa maso Yamma.
Majalisar ta kuma yi Allah wadai da harin da ’yan bindigar suka kai kan jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin, wanda hakan ya yi sanadin salwantar rayukan mutane da dama tare da raunata wasu.
Sanata Uba Sani, dan majalisar daga Jihar Kaduna, wanda shi ne ya gabatar wa majalisar kudurin, ya ce umarnin zai soma aikin ne ba tare da bata lokaci ba.
“Mun ba shugabannin sojoji umarni cewa daga yanzu su yi duk abin da ya kamata, su yi amfani tare da na’urar da muka ba su kudi suka saya domin su yi amfani da ita, don ragargazar ’yan bindigar nan,” inji shi.
Kazalika, majalisar ta koka tare da nuna damuwa kan yadda hukumomin tsaro suka rage yawan jami’an tsaron da ke sintiri a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Majalisar ta sake jadadda wa jami’an muhimmancin kare rayukan al’ummar kasar nan kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanadar.
“Yau idan ka tashi daga Kaduna za ka zo Abuja ko daga Abuja za ka je Kaduna, sai ka yi tafiyar kilomita daya ba ka ga jami’in tsaro ko daya ba sai daji.
“Mun yanke hukunci za mu sake gayyato Manyan Hafsoshin Tsaro don su mana bayanin dalilan da suka rage adadin jami’an tsaron da ke sintiri a hanyar,” cewar Sanata Uba.
Wannan shi ne karo na farko da majalisar ta taba yin yunkurin daukar wani mataki kan hare-haren da ’yan bindiga ke kai wa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.