Kwamatin Kula da Kadarorin Gwamnati da aka yi watsi da su na Majalisar Wakilai ya bukaci hukumar yaki da cin hanci (EFCC) ta gaggauta siyar da kadarorin da aka kwato daga barayin gwamnati.
Shugaban Kwamatin, Ademorin Kuye, ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis.
- ’Yan bindiga sun kashe dan sanda sun kona caji ofis a Binuwai
- An gayyaci golan Enyimba zuwa Super Eagles
Kuye, ya ce matsawar EFCC za ta ci gaba da rike kadarorin a ba ta siyar da su ba, darajarsu za ta rage kuma hakan ba zai amfanar da kasar komai ba.
Shugaban Kwamitin ya ce Gwamnatin Tarayya ta ce za ta cike gibin wani bangare na kasafin shekarar 2021 da kudaden da aka samu daga siyar da kadarorin da aka karbo daga barayin gwamnati.
Kuye, ya ce ci gaba da ajiye kadarorin zai shafi kasafin kudin, sannan ya kuma bukaci EFCC cewa lallai ta fara shirin siyar da su ko kuma Majalisa ta sanya su a kasuwa.