Majalisar Dattawa ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tsawaita wa’adin daina karbar tsofaffin takardun kudi zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2023.
A ranar 15 ga watan Disamba CBN ya fara fitar da sabbin takardun kudi na N200, N500 da kuma N1,000, bayan sanya 31 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar daina karbar tsofaffin takardun kudin.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Tabbatar Da Zaman Lafiya A Harkokin Zabe
- Mata 7 sun kone kurmus a hatsarin mota a Abekuta
Wannan na zuwa ne bayan da kudurin da Sanata Ali Ndume daga Jihar Borno, ya gabatar a zauren Majalisar a ranar Laraba.
Ndume ya soki wa’adin da CBN ya sanya tun farko, inda ya ce kawo yanzu mutane ba sa samun sabbin takardun kudin a cikin birane ballantana kuma mutanen karkara.
Ya ce idan CBN bai tsawaita wa’adin daina karbar tsofaffin takardun kudin ba, hakan na iya jefa miliyoyin mutane cikin wahala.
A baya-bayan nan dai CBN ya fito da tsarin takaita cire tsabar kudi, wanda ya sha suka daga majalisar wakilai da ma daidaikun jama’a.
Hakan ya sanya majalisar gayyatar Gwamnan CBN, Godwin Emefiele don yi mata dauraya kan tsarin, sai dai gwamnan ya kasa bayyana a gabanta kan dalilan rashin lafiya.
Daga bisani CBN ya kara yawan tsabar kudin da mutane za su iya cirewa a mako daga 100,000 zuwa 500,000; kamfanoni kuma daga N500,000 zuwa N5m