✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta bukaci CBN ya tilasta amfani da kudaden tsaba

An dauki shekaru da yin watsi da kudaden tsaba a Najeriya.

Majalisar Wakilai ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya tilasta dawo da yin amfani da kudaden tsaba a Najeriya.

Majalisar ta bayyana cewa yin hakan zai kawo karshen matsalar hauhawar farashin kayan masarufi da ake fama da shi da kuma kawo daidaituwar tattalin arzikin kasar.

Umarnin Majalisar Wakilai na zuwa ne bayan kudurin da dan majalisa mai wakiltar Toro daga Jihar Bauchi, Honorabul Umar Lawal, ya gabatar a zauren Majalisar ranar Talata.

Kudirin ya kuma bukaci CBN ya kafa dokar yin amfani da kudaden na tsaba domin farfado da tattalin arziki.

Dan majalisar ya yi kan yadda a Najeriya aka jima da yin watsi da amfani da kudaden tsaba wanda hakan, a cewarsa, ya haifar da koma bayan tatalin arziki da ake fama da shi a yanzu.

A watan Fabrairun 2007, lokacin Sanusi Lamido Sanusi na Gwmanan CBN, ya sake dawo da amfani da kudaden tsaba, inda aka sabunta su bayan shafe shekaru da yin watsi da su.

Tun a wancan lokaci masana tattalin arziki ke ganin daina amfani da kudaden na iya ta’azzara abubuwa, musamman ta fuskar tattalin arzikin kasa.