✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta amincewa Ganduje karbo bashin Naira biliyan 50

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da rokon da Gwamnan jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya yi mata domin karbo bashin Naira Biliyan 50 domin…

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da rokon da Gwamnan jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya yi mata domin karbo bashin Naira Biliyan 50 domin karasa wasu manyan aiyuka a jihar.

Majalisar ta amince da bukatar ta Gwamnan ne a yayin zaman majalisar na ranar Laraba wanda Shugaban Majalisar Alhaji Abdul’!azeez Garba Gaffasa ya jagoranta.

Da yake karin haske Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Kabiru Hassan Dashi ya bayyana cewa duba da yadda darajar man fetur ta fadi a kasuwar duniya sakamakon bullar cutar coronavirus, ya zama dole gwamnatin ta nemo wasu hanyoyin na samun kudi don ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa da fadin jihar.

A cewar Kabiru Dashi za a biya bashin ne tsawon shekaru 10.

Har ila yau Majalisar ta dage zamanta zuwa makonni biyu inda ta bukaci membobinta da su koma mazabunsu don ci gaba da yin addu’o’in neman tsari daga cutar coronavirus tare da wayar wa am’ummarsu kai game da hanyoyin da za a bi wajen dakile cutar a tsakanin am’umma.