Majalisa Dattawa ta amince da nadin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi na alkalai takwas na Kotun Koli.
Majalisar ta amince da nadin ne bayan ta saurari rahoton kwamitinta na Shairi’a da Kare Hakkin Bil’Adama, da Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti) ya gabatar.
- Majalisa ta fara aiki kan kasafin 2021
- Dole a kori hafsoshin tsaro —Dattawa Arewa
- Buhari da Osinbajo za su ci abincin N167m a 2021
“Idan aka tabbatar da nadin, dukkannin yankunan siyasan kasar nan za su samu alkalai uku da ke wakiltansu sai dai yankin Arewa ta tsakiya wanda zai ci gaba da samun wakilcin alkalai biyu a Kotun Kolin Najeriya.”
Bamidele ya ce, “Arewa ta tsakiya zai ci gaba da za da alkali biyu ne sakamakon mayar da sunan daya daga cikin alkalan da aka gabatar da kwamitin ya yi ga Hukumar Kula Harkokin Shari’a tare da bukatar hukumar ta sake yin nazari.”
Ya kara da cewa yayin da ake yin dukkan mai yiwuwa daomin ganin an cike adadin Alkalin Kotun Kolin, nadin alkalan guda takwas namijin kokari ne daga Shugaba Buhari na karfafa kotun domin tunkarar kalubalen karni na 2021.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tura wa majalisa wasikar bukatar amincewarta da ta zabin alkalan da ya yi.
Sabbin Alkalan Kotun Kolin su ne M. Lawal Garba, JCA daga Arewa maso Yamma; Helen M. Ogunwumiju, JCA daga Kudu maso Yamma; Abdu Aboki, JCA daga Arewa maso Yamma; sai I. M. M. Saulawa, JCA daga Arewa maso Yamma.
Sauran su ne Adamu Jauro, JCA daga Arewa ta Gasa; Samuel C. Oseji, JCA daga Kudu maso Kudu; Tijjani Abubakar, JCA daga Arewa maso Gabas; da kuma Emmanuel A. Agim, JCA daga Kudu maso Kudu.
Sanata Bamidele, a lokacin da yake gabatar da rahoton, ya ce, alkalan da aka zaba sun cika dukkannin shuruddan da ya kamata su cika, kamar yadda sassa na 230 (2) da 231 (1) da (2) da (3) na Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya tanada.
Ya ce alkalan na da zurfin karatun da mutumci da iya shugabancin da ake bukata tare da sanin makamar aikin shari’ar Kotun Koli.
A jawabinsa, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, ya taya su murna tare da yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar an wadatar da Ma’aikatar Shari’a da kudade domin gudanar da ayyukanta yadda tsarin mulki ya tanadar.