Majalisar Dattawa ta amince da dokar halasta tsayawa takarar zabe ba a karkashin kowace jam’iyya ba a Najeriya.
Amincewar Majalisar da kudurin zai ba wa daidaikun mutane masu cin gashin kansu damar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa da gwamnaoni da shugabancin kananan hukumomi ko wakilici a majalisar dokoki ba tare da jam’iyya ba.
- Yadda da ya yi dambe da ’yan bindiga ya kwaci mahaifinsa a Kano
- Jami’in EFCC ya mutu a wurin fada da abokan aikinsa
A zaman majalisar ta ranar Talata, ta kuma amince da kudurin dokar sanya Shugaban Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai a cikin mambobin Kwamitin Tsaro na Kasa.
Ta kuma umarci Akawun Majalisar Dokoki ta Kasa da ya gabatar da kudurorin biyu da ta kammala karatu da kuma amince da shi ga Shugaba Muhammadu Buhari, domin sanya hannu.
Wannan dai na zuwa ne mako biyu kafin karewar wa’adin majalisar da shi kansa Shugaba Buhari.
Dokokin biyu na daga cikin sauye-sauyen da aka yi wa kundin tsarin mulki da aka aike wa Fadar Shugaban Kasa a karshen shekarar da ta gabata.