✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta amince a gina sabbin jami’o’in kiwon lafiya guda 6 a Najeriya

Za a kafa su ne a kowacce daga cikin shiyyoyin siyasar Najeriya guda shida

Majalisar Dattijai a ranar Talata ta amince da wani kuduri da ke neman kafa Jami’ar Kiwon Lafiya da Fasaha a kowace daga cikin shiyyoyin siyasar kasar nan guda shida.

Hakan dai ya biyo bayan nazarin rahoton da Kwamitinta na Lafiya a Manyan Matakai, karkashin Sanata Yahaya Oloriegbe (APC, Kwara), ya gabatar a zauren Majalisar.

Sanata Yahaya, yayin da yake gabatar da rahoton, ya ce gina sabbin jami’o’in zai magance karancin guraben karatun da ake fuskanta ga daliban da ke neman karantar fannin likitanci da sauran kwasa-kwasan kiwon lafiya a Najeriya.

Ya kuma ce makarantun za su samar da isassun ma’aikatan lafiyar da kasar ke bukata su kuma bunkasa samar da ayyukan yi da habaka tattalin arzikin kasa.