Sanata Ali Ndume ya ce Shugaba Tinubu da kansa ya bukace shi ya jagoranci yakin neman zaben Sanata Godswill Akpabio a takarar shugabancin Majalisar Dattawa ta 10.
“Shugaban kasa ya fada min cewa Sanata Akpabio ne dan takararsa kuma ya kamata na jagoranci yakin neman zabensa,” in ji Ndume a hirarsa da gidan talabijin na Channels.
- Tinubu ya umarci a fara shirin rage radadin cire tallafin mai
- NAJERIYA A YAU – Shin Buhari Zai Iya Rayuwa A Daura?
Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa shugaban kasa ba zai sauya matsayinsa kan shugabancin Majalisar Dattawa ta 10 ba.
A cewar Ndume, wanda ya shekara 20 a majalisar dokokin kasar nan, daga cikin zababbun Sanatoci 109 a majalisar, 75 ne sun nuna goyon bayansu ga Akpabio.
“A yanzu haka muna da sanatoci 75 kuma duk alamun nasara na tare da mu. Muna da goyon bayan jam’iyya da shugaban kasa, da kuma mafi muhimmanci, goyon bayan akasarin sanatoci kuma sun sanya hannun amincewa da tsarinmu,” in ji shi.
A watan Mayu ne Jam’iyyar APC ta ware wasu manyan mukamai hudu na Majalisar Dattawa ta 10 tare da bayyana zababbun ’yan majalisar da take so su rike su.
Tsarin shiyya-shiyyar da aka yi shi ne kamar haka:
- Shugaban Majalisar Dattawa – Kudu maso Kudu – Sanata Godswill Akpabio (Akwa Ibom)
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa – Arewa maso Yamma – Sanata Barau Jibrin (Kano)
- Shugaban Majalisar Wakilai – Arewa-Maso-Yamma – Abass Tajudeen (Kaduna)
- Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai – Kudu maso Gabas – Ben Kalu (Abia).
Ndume, ya bayyana cewa du da cewa “Ana iya samun wadanda za su su sauya ra’ayi daf da karshe, amma ina da kwarin gwiwa. Ba na so na kasance mai yin gaba-gadi saboda mutane na iya sauya ra’ayinsu, amma dan takararmu shi ne mafi nagarta.
“Akwai ’yan takara biyu da ke kan gaba a yanzu, wato Yari da Akpabio kuma, amma dan takararmu yana da duk wata fa’ida fiye da sauran ’yan takarar, a siyasance da kuma tunani, muna sa ran nasara,” in ji Ndume.