✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta 10: Ba mu tsara yadda za mu raba mukamai ba —Abdullahi Adamu

Shugaban APC na Kasa, Abdullahi Adamu, ya ce ba gaskiya ba ne maganagnun da ke yawo cewa jam’iyyarsu ta gama tsara shiyoyiyn da za su…

Shugaban APC na Kasa, Abdullahi Adamu, ya ce ba gaskiya ba ne maganagnun da ke yawo cewa jam’iyyarsu ta gama tsara shiyoyiyn da za su jagoranci Majalisar Tarayya ta 10.

Adamu ya bayyana hakan ne a ganawarsa da manema labarai bayan kada kuri’arsa a Keffi da ke Nasarawa ranar Asabar, kan rahotannin da ke yawo cewa APCn za ta mika shugabancin majalisar dattijai ga yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ya  kuma ja hankalin ’yan siyasa da su dakaci sanarwar jam’iyyar a hukumace ba wai jita-jita ba.

“Rahotan bai wa wata shiyya shugabancin majalisa zance ne kawai, ba mu bai wa kowa ba.

“Na fada sau shurin masaki tun ranar Litinin, kuma zan sake maimaitawa, ba mu tsaida kowa ba har yanzu”, in ji shi.

Shi ma dai Sakataren Yada Labaran APC Felix Morka ya musanta batun.