Majalisar Dattawa na zargin Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) da kin sanya N1.4bn na harajin ta ta karba daga ma’aikatu da hukumomi (MDAs) a asusun Gwamnatin Tarayya.
Tuhumar na kunshe ne a rahoton binciken shekarar 2015-2020 da Babban Oditan Tarayyar ya gabatar wa Kwamitin majalisar kan asusun gwamnati wanda Sanata Mathew Urhoghide ke jagoranta.
- Gwamnatocin jihohi za su samu tallafi don yafe haraji
- Majalisa ta caccaki hukumomin haraji kan biliyan 58
- FIRS da NIPOST na cacar baki kan kudaden haraji
“An bukaci Shugaban FIRS da a cire WHT din da ba a cire ba na N700.2 miliyan daga kasafin MDAs da abin ya shafa kamar dokar FIRS ta 2007 ta tanadar.
Rahoton ya ce an ciri kudaden da kasafin hukumomin amma ba a tura wa FIRS ba.
Hakan ya karya dokar kudi mai lamba 234 (III), ga duk jami’an da suka kasa cire harajin VAT da WHT, kuma za a sanya musu takunkumi a karkashin dokar VAT mai lamba 102 na 1993 wacce ta hada da tara ko dauri.
Ya kara da cewa za su shawarci Ankata Janar na kasa a kan a cire kudaden daga cikin kasafin karkashin sashi na 24 na dokar FIRS.
Rahoton ya kuma ce an cire N708.5m na kudin haraji daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati 31 amma ba a tura wa FIRS a rubuce ba.