✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa na son sabon Hafsan Sojin Kasa ya magance matsalar tsaro

Sabon Hafsan Sojin ya bukaci hadin kan jama'a don kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Majalisar Wakilai ta bukaci sabon Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Manjo Janar Faruk Yahaya, da ya magance matsalar tsaron da ta addabi kasar.

Mambobin majalisar sun ba da shawarar ne a ranar Talata lokacin gabatar da sunan sabon hafsan, yayin da ya bayyana gaban Kwamitin Tsaro don tantancewa da shi.

  1. Masu garkuwa sun harbe direba, sun sace uwa da danta a Nasarawa
  2. Rashin tsaro: Aisha Buhari ta bukaci daukar karin jami’an tsaro

Shugaban Kwamitin Majalisar kan Harkokin Tsaro, Babajimi Benson ne ya shugabanci kwamitin tantancewar tare da Shugaban Kwamitin Majalisar kan Sojoji, Abdulrazaq Namdas.

Bayyanar Janar Yahaya, ta biyo bayan takardar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya aike wa da majalisar don bukatar tabbatar da shi a makon da ya gabata.

Bukatar na zuwa ne bayan rasuwar tsohon Babban Hafsan, Ibrahim Attahiru a hatsarin jirgin sama a Kaduna a watan da ya gabata.

Da yake jawabi yayin bude taron, shugaban kwamitin, Babajimi Benson ya ce nadin nasa ya zo a wani lokaci mai matukar wahala a tarihin kasar.

Ya ce Najeriya na fuskantar kalubale da dama na tsaro na siyasa, ‘yan bindiga, masu tayar da kayar baya, da masu neman ballewa daga kasar.

Ya kuma ce, “Mafi munin shine tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabas. Wannan yakin ya jawo wa kasa asara mai dimbin yawa. Dole ne mu kawo karshen hakan.

“Sojojin Najeriya na bukatar sabbin dabaru don dakile kashe-kashe da barnata dukiya ba dalili sakamakon wadannan lamura na rashin tsaro.

“Don haka, ina fata, idan har an tabbatar da shi, sabon Hafsan Sojin zai yi duk mai yuwuwa, tare da aiki da sauran shugabannin rundunoni, don kawo karshen wannan,” in ji shi.

Shi kuwa sabon Babba Hafsan Sojin, Manjo-Janar Faruk Yahaya cewa ya yi ya kasance  cikin aikin sojin Najeriya tsawon shekaru 36 kuma yana da cikakkiyar kwarewa a cikin wadannan shekarun.

Ya ce, “Na yi imanin ina da abubuwan da ake bukata, don gabatar da aikina  a wannan ofishin na Babban Hafsan Sojin Kasa in har an tabbatar da ni.

“Harkar tsaro abu ne da ya shafi kowa, ba aikin mutum daya bane. Don haka muna  bukatar tallafi da hadin kan jama’a don kawo karshen matsalar,” inji shi.