✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa na so a fara ba masu ‘first class’ aiki da zarar sun kammala digiri

Majalisar ta ce hakan zai taka rawa wajen karfafa gwiwar matasan

Majalisar Wakilan Najeriya ta yi kira ga hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya da su fara bayar da ayyukan yi kai tsaye ga duk matashin da ya kammala karatun digiri da shaidar karatu mai daraja ta farko, wato ‘first class’.

Bukatar hakan ta biyo bayan wani kuduri da dan majalisar, Chinedu Emeka ya gabatar a gabanta ranar Laraba, inda ya ce jami’o’i na samar da daruruwan matasa masu first class din a kowace shekara wadanda suke shan wahala wajen samun ayyuka.

A cewarsa, lamarin ya sa matasan da dama yin tururuwa wajen barin kasar nan, inda suke barin masu sakamako mara kyau, wadanda ke da hanyoyi wajen samun aiki, inda ya ce hakan na matukar yi wa kasar illa.

Dan majalisar ya ce matukar kasar ba ta samo hanyoyin saka wa zakakuran matasa ba, za ta jima tana zaune a matsayin koma baya.

Majalisar ta kuma bukaci Ma’aikatar Ilimi da ta hada gwiwa da sauran hukumomin gwamnati don tabbatar da an sama wa matasan mafita.

Daga nan sai Majalisar ta tilasta wa Kwamitocinta na Manyan Makarantu da na Samar da Ayyukan yi don tabbatar da ganin an bi dokar.