✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ba ta amince da sayan sabbin jiragen shugaban ƙasa ba — Akpabio

Ya ce majalisar har yanzu ba ta amince da buƙatar saya wa Shugaban ƙasa sabbin jirgi ba.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce majalisar ba ga amince a saya wa Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sabbin jiragen hawa.

Akpabio ya yi watsi da wani rahoto da ke nuna cewa majalisar za ta amince da sayen sabbin jiragen sama ga Shugaba Tinubu da Shettima, bayan matsin rayuwa da ake fama da shi a Najeriya.

Rahoto ya biyo bayan shawarar da kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaro ya bayar, na sayen sabbin jiragen sama saboda matsalolin da jiragen shugaban ƙasa ke fuskanta.

A wata sanarwa da mai taimaka wa Akpabio kan harkokin yaɗa labarai, Jackson Udom ya fitar, ya musanta cewa majalisar ta amince da ƙudirin samar da sabbin jiragen saman.

Ya bayyana cewar shugaban majalisar, yana Jihar Borno wajen ta’aziyyar rasuwar mahaifin Sanata Tahir Monguno.

Akpabio ya ce raɗe-raɗin ba komai ba ne, face farfaganda da kuma labarin ƙanzon kurege.

A gefe guda kuma, ya bayyana gamsuwarsa game da sha’anin tsaro a Jihar Borno, inda ya yi addu’ar ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.