✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mairo Mandara: Fafutuka don sama wa al’umma lafiya

Dokta Mairo Mandara ta dade tana fafutuka a bangaren kiwon lafiya a ciki da wajen Najeriya

Dokta Mairo Mandara likitar mata ce, kuma kwararriya a harkar kiwon lafiyar al’umma da dabarun sauya rayuwar al’umma.

Ta yi aiki da kungiyoyi da hukumomi masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya na gida Najeriya da na kasa-da-kasa.

Sannan ta yi aiki da manyan jami’an gwamanti, da shugabannin al’umma da na addini, da kungiyoyin mata da na sa-kai a sassan Afirka daban-daban.

Hukumomi ko kungiyoyin da ta jagoranci rassansu a Najeriya sun hada da Gidauniyar Bill & Melinda Gates  da Gidauniyar Packard da sauran su.

Tauraruwar Arewa maso Gabas

A yunkurinta na kawo sauyi a rayuwar mata da yara mata, ta kirkiri kungiyar Girl Child Concerns mai fafutukar inganta rayuwar mata da yara mata. Ita ce kuma Shugabar Hukumar Amintattu ta kungiyar.

Kungiyar kan samar da hanyoyin samun ilimi ga mata da koyar da dabarun tsira da mutunci ga ’yan mata, musamman wadanda aka yi musu aure suna da kananan shekaru.

Wata rawa da Dokta Mairo Mandara take takawa a irin wannan fafutuka ita ce shiga da ta yi ana damawa da ita a yunkurin sake gina shiyyar Arewa maso Gabas, wadda rikicin Boko Haram ya daidaita a shekaru 10 da suka gabata.

Ilimin ’ya’ya mata

A wannan shiyyar, Tauraruwar tamu tana fafutukar ganin an bai wa ’ya’ya mata ingantaccen ilimi, sannan an sama wa mata sana’o’in da za su yi don su farfado da martabarsu.

Dokta Mairo Mandara babbar malama ce amma ba ta dindindin ba a fannin cututtukan mata a Jami’ar Maiduguri da Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.

Tauraruwar mamba ce a Kwamitin Tantance Ingancin Manyan Cibiyoyin Lafiya na Kasa da Kwamitin Garambawul ga Bangaren Kiwon Lafiya a Najeriya, wanda Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo yake jagoranta.