Iyalan Tsohon Shugaban Kwamitin Shugaban kasa na Gyaran Fansho, Abdulrasheed Maina sun ce tsohon shugaban kwamitin fanshon wanda aka kora daga aiki zai bayyana idan gwamnati ta basu tabbacin tsaron lafiyarsa.
Iyalan nasa sun bayyana haka ne a taron manema labarai da suka kira a Kaduna a ranar Laraba.
“Kamar yadda kuka sani a baya an yi ta kai wa Maina hari, saboda haka darasin da muka samu a baya ya koya mana darasi amma idan aka ba mu tabbacin tsaron lafiyarsa zai bayyana daga inda yake kuma ya gayawa ’yan Najeriya gaskiya”. Inji Mai Magana da Yawun Iyalansa, Aliyu Maina