✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mailafia zai sake bayyana a gaban DSS

Lauyansa ya ce gayyatar Mailafia na da alaka da ganawar da ya yi da DSS makon jiya

Da karfe 12 na ranar Litinin ne ake sa ran tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Obadiah Mailafia, zai sake bayyana a ofishin Hukumar Tsaro ta DSS da ke Jos, babban birnin Jihar Filato.

Lauyan Dokta Mailafia, Yakubu Bawa, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) hakan.

Lauyan ya kuma ce sabuwar gayyatar na da nasaba da ganawar Mailafia da hukumar a makon jiya.

“Ina ganin ba wani abu ba ne na daban da ganawarsa ta farko da DSS, wadda ta musayar ra’ayi ce kawai”, inji shi.

Idan ba a manta ba, ranar Larabar makon jiya ce hukumar DSS ta gayyaci Mailafia bayan wata tattanawa da ya yi da gidan rediyon Nigeria Info da ke Abuja.

Yayin tattaunawar dai Mailafia ya yi zargin cewa daya daga cikin gwamnonin arewa na mara wa Boko Haram.

Daga bisani hukumar ta saki tsohon Mataimakin Gwamnan na CBN bayan an kwashe sa’o’i shida ana yi masa tambayoyi.

Hukumar dai ta fitar da sanarwa tana cewa Dokta Mailafia ya yi nadamar abubuwan da ya fada har ya nemi afuwa, shi kuma ya ce yana nan a kan bakanshi.