✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maikaba ya yi ban-kwana da kocin Wikki Tourists

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist ta Bauchi, Abdu Maikaba ya ajiye aikinsa a kulob din kuma yanzu haka ana hasashen zai koma kulob…

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist ta Bauchi, Abdu Maikaba ya ajiye aikinsa a kulob din kuma yanzu haka ana hasashen zai koma kulob din Abia Warriors don ya ci gaba da horarwa a can.
Sai dai akwai rahotannin da suka nuna Maikaba yana shirin sanya wa kulob din Sunshin Stars na Akure hannu ne bayan da Kocinsu Kennedy Boboye ya ajiye aiki.  Amma bayanai na baya-bayan nan sun nuna Maikaba yana shirin komawa kulob din Abia Warriors ne bayan da kocinsu Ladan Bosso shi ma ya ajiye aikin horarwa.
Wata majiya da ta kyankyasa wa kafar sadarwar wasanni ta africanfootball.com ta tabbatar da cewa , Maikaba ya yi ban kwana da Wikki Tourist  kuma yanzu haka yana yunkurin komawa kulob din Abia Warriors don ya ci gaba da horarwa a can.
Tsohon kocin din Enyimba da Kano Pillars, Abdu Maikaba ya samu yabo a kakar wasan kwallon kafa da ta wuce bayan ya taimaka wa kulob din Wikki Tourist  inda kulob din ya gama a matsayi na hudu a gasar rukunin firimiya ta Najeriya duk da matsalar kudi da kuma ta ’yan wasa da ta dabaibaye kulob din.