kasar Afirka ta Kudu ta nuna aniytarta na daukar gasar wasannin Olamfik wanda za a gudanar a shekarar 2024 watau nan da shekaru goma masu zuwa idan Allah Ya kaimu.
Haka kuma kasar ta nuna sha’awarta na daukar nauyin gasar wasanni ta kasashe renon Ingila da ake wa lakabi da Commonwealth Games a shekarar 2022 watau shekara biyu kafin gasar Olamfik..
Misnitan kula da harkokin wasanni na kasar mai suna Fikile Mbabula ne ya sanar da haka a ranar Talatar da ta wuce a lokacin da yake zanawa da jaridar Business Day.
“Harkokin wasanni suna bunkasa cigaban kasa musamman ta bangaren gine-gine”, inji Ministan a lokacin hira da manema labarai.
A shekara mai zuwa (2015) ce ake sa ran Kwamitin shirya wasan Olamfik zai bude kafa ga kasashen da ke bukatar daukar nauyin gasar su gabatar da bukatunsu game da yin hakan. Sannan a shekarar 2017 ce ake sa ran kwamitin zai sanar da kasar da aka zaba wacce za ta dauki nauyinta a shekarar 2024. Don haka Afirka ta Kudu ta fara shirye-shiryen shiga sahun kasashen da za su yi takara a badi wajen neman daukar nauyin gasar.
Za a gabatar da gasar Olamfik ta shekarar 2016 ce a Rio de Janeiro da ke Brazil yayin da za a gabatar da ta 2020 a Tokyo da ke Japan.
Idan za a iya tunawa Afrika ta Kudu ce ta dauki nauyin gasar cin kofin kwallo na duniya a shekarar 2010 kuma an kiyasta ta kashe fiye da Dala biliyan 3 kimanin Naira biliyan 465 wajen samar da gine-ginen da aka yi amfani da su yayin gasar.
Mai yiwuwa Afirka ta Kudu ta dauki nauyin gasar Olamfik a 2024
kasar Afirka ta Kudu ta nuna aniytarta na daukar gasar wasannin Olamfik wanda za a gudanar a shekarar 2024 watau nan da shekaru goma masu…