✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mai ’ya’ya 8 na neman a raba aurenta na shekaru 19 saboda rashin abinci

Matar dai ta roki kotun ta sauwake mata auren da ta shafe kimanin shekaru 19 tana tare da mijinta

Wata matar aure mai kimanin shekaru 38 a duniya, Hafsat Mu’azu ta garzaya gaban wata kotun Shari’ar Musulunci dake Rigasa Kaduna tana neman a raba aurenta da mijinta saboda rashin abinci.

Matar dai ta roki kotun ta sauwake mata auren da ta shafe kimanin shekaru 19 tana tare da mijinta mai suna Ishaku Aliyu.

Hafsat wacce take da ’ya’ya takwas da mijin nata ta ce ta jima tana hakuri da shi ne kawai saboda yaran da suka Haifa tare, amma yanzu ta ce tura ta kai bango.

A cewarta, hakurinta ya kare saboda ko kadan mijin nata ba ya ganin girmanta.

Sai dai a nasa bangaren, mijin ya musanta dukkan zarge-zargen da matar take yi masa, inda ya bayyana su a matsayin kanzon kurege.

Daga nan ne sai alkalin kotun, Mai Shari’a Malam Salisu Abubakar-Tureta ya tambayai matar ko tana da hujja inda ta ce eh.

Daga nan sai ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu mai zuwa domin matar ta gabatar da hujjjinta.