✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mai taimaka wa IPOB da kudade daga kasar waje ya shiga hannu

Dubunsa ta cika bayan ya tura wa haramtacciyar kungiyar kudade daga kasar waje.

’Yan sanda sun cika hannu da mutumin da ke taimaka wa haramtacciyar kungiyar IPOB mai neman ballewa daga Najeriya da kudade daga kasashen waje.

Dubun mutumin ta cika ne bayan na ya tura wa IPOB Naira miliyan 10 daga kasar waje ne, inda ’yan sanda suka yi ta bibiyar shi, har suka cafke shi a garin Orlu na Jihar Imo.

Yankin Orlu na daga cikin wuraren da IPOB ta kai ta tsananta kai hare-hare kan cibiyoyin tsaro, har ta kashe ’yan sanda da dama ta kona ofisoshinsu da wasu gine-gine gwamnati a kwanakin baya.

Sanarwar da kakakin Rundunar, CSP Mike Abattam, kan mutumin da ke fuskantar zargin ta’addanci ta ce, “Da muka titsiye shi ya amsa cewa ya taimaka wa IPOB da bangaren sojin kungiyar (ESN) da Naira miliyan 10 a lokacin yana kasar waje.

“Ya kuma taimaka wa ’yan sanda wajen cafke wasu mambobin kungiyar tare da tarwatsa maboyarsu a Jihar.

“Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Imo, CP Abutu Yaro, ya yaba wa al’ummar Orlu da ma daukacin jihar, yana mai kira gare su da su kwantar da hankalinsu domin hukumomin tsaro na yin iya kokarinsu domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a fadin jihar”.