Wani mummunan lamari na kisan gilla ya afku a ƙauyen Galadanchi da ke Ƙaramar hukumar Dutse a Jihar Jigawa.
Rundunar ’yan sandan jihar ta kama wani tsoho mai shekara 70 bisa zargin kashe ƙanwarsa saboda rikici kan filin gado.
- Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu
- An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a Borno
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar y’an sandan jihar, SP Lawan Adam Shi’isu ya fitar ya ce tsohon mai suna Adamu Yakubu – ɗan asalin ƙauyen Galadanchi ne wanda ya samu saɓani da ƙanwarsa mai suna Hannatu Hashimu, mai shekara 45, kan rabon gadon wata gona da suka gada.
Bayanan binciken farko da ’yan sanda suka fitar, ya nuna cewa wanda ake zargin ya jefi ƙanwar tasa da sanda ne a lokacin da suka yi zazzafar gardama a tsakaninsu kan rabon gadon.
Rikicin dai ya fara ne kamar da rashin jituwar musayar kalamai, amma ya rikiɗe zuwa tashin hankali.
Inda tsohon da ake zargin ya kai wa ƙanwar tasa duka da sanda, wanda ya yi sanadin mutuwar Hannatu Hashimu. Kamar yadda bayanan ’yan sanda ya nuna.
”Marigayiyar ta fita daga gidan a fusace, ta koma gidan aurenta, da zuwanta kuma ta faɗi ta suma, nan take aka garzaya da ita asibiti inda likitocin Babban Asibitin Dutse suka tabbatar da mutuwarta”, cewar ’yan sandan.
Rundunar ’yan sandan sun kama tsohon da ake zargin, inda yanzu haka suke gudanar da bincike.