✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai shekara 60 ya yi wa karamar yarinya fyade

Iyayen yarinyar sun shigar da kara kan zargin da suke yi wa tsohon.

Hukumar tsaro ta NSCDC ta cafke wani mai shekara 60 kan zargin yi wa yarinya mai shekara tara fyade a Jihar Kwara.

Wannan na dauke ne cikin sanarwar da kakakin hukumar a Jihar, Babawale Afolabi, ya fitar a ranar Asabar cewa an shigar da kara kan tsohon.

“A ranar Juma’a 28 ga Mayu, 2021 iyayen yarinyar suka shigar da kara kan fyade da tsohon ya yi wa ’yarsu.

“Tsohon ya ribaci yarinyar ta hanyar ba ta kyautar N50, kuma ya amsa laifin da ake tuhumar sa da aikatawa.

“An kai yarinyar asibiti za a duba lafiyarta tare da ba da rahoton faruwar lamarin.

“Ana ci gaba da bincike kan lamarin a hedikwata, wanda ake zargin kuma za a kai shi kotu da zarar an kammala bincike,” a cewar Afolabi.

Matsalar yi wa kananan yara fyade na barazana garesu da iyayensu, duk da cewar gwamnati na fadi-tashin ganin an kawar da dabi’ar, amma haka ba ta cimma ma ruwa ba.