✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai sharar titi ta gano maboyar masu garkuwa da mutane a Legas

Da safiyar ranar Talatar da ta gabata ne wata mata da ke aikin sharar titi da ke aiki da gwamnatin jihar Legas ta gano inda…

Da safiyar ranar Talatar da ta gabata ne wata mata da ke aikin sharar titi da ke aiki da gwamnatin jihar Legas ta gano inda musu garkuwa da mutane suke boye jama’a a karkashin wata babbar magudanar ruwa da ke yankin Ijaiye de ke kan tsohuwa babbar hanyar Abekuta zuwa Legas.
Matar mai matsakaicin shekaru wacce ake kira Misis Munirat Aduke ta ce lamarin ya auku ne yayin da ta fito da sanyin safiyar ranar don ta fara aikinta na shara.
Ta ce  da misalin karfe tara na safe kwatsam sai ta ji wata murya daga cikin magudanar ruwan na kiran a kawo mata agaji.
Ta ci gaba da cewa da ta matsa kusa da wurin da take jin sautin muryar sai ta ga cewa muryar tana fitowa ne daga cikin magudanar ruwan.
“Da na leka cikin magudanar ruwan don na ga abin da ke faruwa sai na ga kimanin mutane hudu a ciki. Sai kawai na ji muryar namiji kuma tana gargadina kada na kuskura na matso wurin. Sai na yi gaggawar kiran wasu jami’an ’yansanda wadanda ke aiki a wani banki da ke kusa da wurin, da suka zo, sun yi kokarin su ceci wadanda suke ciki amma sai suka fuskanci tirjiya daga daya daga cikin mazan da ke cikin ramin inda ya rika jifansu da duwatsu”. Inji ta.
Ta kara da cewa da ’yansanda suka ga lamarin ya fi karfinsu sai suka nemi agajin karin jami’ai na musamman.
“Da aka turo karin jami’an ’yansanda, sai suka fara ceto daya daga cikin matan sai kuma suka ceto wani mutum daga bisani kuma suka fito da daya daga cikin masu garkuwa da mutane karfi da yaji daga cikin ramin”. Inji ta.