✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai shafe minti 6 yana fesar da ruwa daga baki

Fesar da ruwa tsohuwar dabara ce da ta samo asali tun Ƙarni na 17.

Wani ɗan ƙasar China mai suna Ma Hui mai shekara 35 ya kafa sabon tarihi a Kundin Tarihi na Duniya (Guinness) kan fesar da ruwa daga bakinsa a-kai-a-kai har tsawon minti 5 da daƙiƙa 51.88.

Fesar da ruwa tsohuwar dabara ce da ta samo asali tun Ƙarni na 17.

Ya ƙunshi shan ruwa mai yawa sannan a sake shi ta amfani da sarrafa ƙarfin jiki.

Ba wani abu ne da kowa zai iya yi ba a fili, amma mun ga wasu kyawawan maɓuɓɓugan ruwa na ɗan Adam a cikin shekaru.

Duk da haka babu wanda ya kai bajintar Ma Hui, da ya kafa sabon tarihin tsawon lokaci yana fesar da ruwa daga bakinsa.

Idan aka ce bai karya tarihin wasu a baya ba, zai zama rashin fahimta, duba da cewa ya yi nasarar fesar da ruwa daga bakinsa na kusan minti shida, yayin da wanda ya riƙe da kambun ɗan ƙasar Habasha mai suna Kirubel Yilma, ya yi hakan na daƙiƙa 56.36 kacal.

Don samun ingantaccen kambun tarihi na Guinness, wanda zai samu sai ya yi ƙoƙarin fitar da ruwa daga bakinsa a-kai- a-kai yana ci gaba da yi.

Da zarar ruwan ya ƙare ko ya tsaya, za a dakatar lokacin da ake naɗa a hukumance ya ƙare.

Don wannan yunƙurin kafa tarihi, Ma Hui ya sha lita 4.5 na ruwa, sa’an nan ya sake fesar da shi a hankali, yana nuna ƙarfin jikinsa mai ban-mamaki.

Mai yiwuwa ba zai yi kama da yana yin abubuwa da yawa ba, amma dabararsa ita ce fesar da ruwan. Ma Hui lokacin da yake fesar da ruwa daga cikin bakinsa