Wani mutumin Afirka ta Kudu mai shekara 22 da yake zaune a kasar Ostireliya ya shiga Kundin Tarihi na Duniya bayan da ya ziyarci mashaya daban-daban har 78 a cikin awa 24.
Mutumin mai suna Heinrich de Billiers ya samu sako daga ofishin Kundin Tarihi na Duniya a ranar 10 ga Nuwamba.
- Wike ya gayyaci Kwankwaso bude ayyukan da ya yi a Ribas
- Kaso 60 na ’yan Arewa ba su da asusun ajiya na banki – Uba Sani
A cikin sakon an bayyana cewa zaryarsa a gidajen shayeshaye ta Fabrairu tare da samun goyon baya daga ayarin da yake kunshe da dan uwansa Ruald de Billiers da abokinsa Wessel Burger, an amince cewa ita ce ziyarar mashaya mafi yawa cikin awa 24 (ta mutum daya).
De Billiers ya kwace kambin ne daga wani dan Ingila mai suna Nathan Crimp, wanda ya ziyarci mashaya 67 a yankin Brighton na kasar Ingila a cikin awa 24.
“Yana da muhimmanci a fahimci cewa a dokar Kundin Tarihi na Duniya ana so mu sha kowane nau’in abin sha mililita 125 a duk inda muka ziyarta,” de Billiers ya shaida wa kafar labarai ta Broadsheet.