Al’ummar Fulani makiyaya mazauna yankin Alata da Idiba, da Iresa a Ƙaramar Surulere a Ogbomosho sun wayi gari da harin wasu ɓata-gari waɗanda suka ƙone gidajensu da ɗaukacin rumbunan abincinsu.
Alhaji Adamu Musa ɗaya daga cikin shugabannin yankin Fulani maƙiyayan ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya samo asali ne daga wani rikici a tsakanin wasu abokan juna da ke shaye-shaye a wata mashaya ta wani otel a cikin garin Ogbomosho.
- Likitoci sun tsayar da ranar shiga yajin aiki a Kano
- Hajjin Bana: Gwamnati ta ɗauki nauyin maniyyata 47 a Ribas
Ya ce, “Wani yaro Bafulatani da aka haife shi a garin da abokansa Yarbawa suna shaye-shaye sai faɗa ya ɓarke a tsakaninsu, wannan Bafullatani sai ya soki abokinsa Bayarabe da wuƙa, cikin dare ranar Litinin.
Da gari ya waye sai wasu maƙwabtanmu Yarbawa suka kira mu ta waya suka faɗa mana akwai wasu mahara za su kawo mana farmaki don haka mu kwashe ’ya’yanmu da matanmu mu gudu.
“Ina zaune ba ni da lafiya, don haka ban iya gudu ba sai mata da yara ne suka gudu, da maharan suka zo duk rugagen da ke wannan yanki sun kunna musu wuta suka kwashe mana kaya har suka iso inda nake nan ma suka sanya wuta cikin ɗakin da nake. A haka matata ta cicciɓe ni don ba na iya tafiya, ta kau da ni daga wajen wutar,” in ji shi.
Ya ce haka suka bar su ba su da komai sun ƙone ɗaukacin kayan abinci da suturarsu kan rikincin da ba su da alaƙa da shi.
“Don haka muna kira ga mahukunta su shigo wannan lamari, su kawo mana ɗauki ko agajin kayan abinci da sutura, kuma a kamo waɗanda suka aikata mana wannan ɗanyen aiki, domin in an bar su gobe ma haka za su yi mana,” in ji shi.
Aminiya ta gano cewa Bafulatanin da aka yi rikicin da shi yana hannun ’yan sanda, yayin da wanda aka soka da wukar ke kwance a asibiti yana jinya.
Da wakilinmu ya tuntuɓi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo, SP Adewale Osifeso, bai amsa waya ba, bai kuma mai do da saƙon kar-ta-kwana da wakilinmu ya aike masa ba har lokacin haɗa wannan rahoto.