Wadansu miji da mata da tsawon kowanensu ya haura kafa shida, su ne ma’auratan da suka fi kowane rukunin ma’aurata tsawo a duniya.
Ma’auratan Mista Sun Mingming da matarsa Xu Yan, dukkansu ’yan Kasar China ne da Kundin Tarihi na Duniya (Guinness World Records) ya tabbatar da cewa su ne ma’auratan da suka fi tsawo a duniya.
- An kama ’yan sandan da suka yi wa budurwa kwace
- Kocin Real Madrid Zidane ya kamu da Coronavirus
- Limaman Kirista sun yaba da wa’azin Sheikh Gumi ga Fulani
Mingming mai shekara 33 yana da tsawon kafa 7 da inci 9 sannan matarsa, Xu Yan mai shekara 29, tsawonta ya kai kafa 6 da inci 1.74.
Idan an hade tsawon ma’auratan biyu zai kai sama da kafa 13 da inci 10.
Ma’auratan sun shahara a fannin wasannin motsa jiki, inda mijin, Mingming ke yin wasan Kwallon Kwando, yayin da matarsa Yan ke wasan Kwallon Hannu.
Ma’auratan sun hadu ne a wata gasar wasanni ta Kasar China da aka yi a shekarar 2009, sannan suka yi aure a birnin Beijing a ranar 4 ga Agustan 2013.
A lokacin da ma’auratan suka ziyarci hedkwatar Hukumar da ke ba da lambar shiga Kundin Tarihi a Birtaniya, sun bayyana murna da farin cikin kan auren juna da suka yi.
“Ba wanda zai komai daidai, don haka akwai bukatar a tallafa wa wani a kullum,” inji Mingming.
Ya bayyana cewa, “A kullum akwai kalubale irin na tafiya a karamar mota, tafiya a cikin jirgin sama ko kuma samun daki a otal, sai an fuskanci matsala saboda tsawon.”