Mai Rusau wani lakabi ne da abokan adawar Gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i suka yi amfani da shi kafin zaben shekarar 2015. Abokan adawar sun yi amfani da wannan lakabi ne domin yarfen siyasa inda suka rika cewa kada jama’ar Jihar Kaduna su zabi Malam Nasir El-Rufa’i a zaben 2015, suna masu cewa idan suka zabe shi zai rusa musu gidajensu, suna kawo misali da rushe gine-ginen da ba a yi su kan ka’ida ba a lokacin da yake Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja. Ganin haka sai bangaren magoya bayansa suka mayar da abin ya zama wani salo na yakin neman zabe inda suka rika mayar da martani da cewa, “A rusa zalunci, a gina adalci.” Haka dai abin ya ci gaba al’ummar Jihar Kaduna suka yi watsi da wancan yarfen siyasa ta abokan adawa suka yi la’akari da irin kokarin da Malam Nasir El-Rufa’i ya yi a lokacin da ya yi Ministan Abuja, inda Abuja ta sauya fasali ta yi kyau ta koma kamar wata karamar Landan.
Bayan samun nasarar zaben Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i a matsayin Gwamnan Jihar Kaduna a shekara 2015 bai yi wata wata ba, ya dauki matakan ganin ya dawo da maratabar Jihar Kaduna kamar yadda yake a manufofin Jam’iyyar APC ta Jihar Kaduna. Sai dai babbar matsalar ita ce jihar ba ta da kudin da za ta aiwatar da wadannan ayyuka. Wannan dalili ya sa Gwamna El-Rufa’i ya dauki wasu matakai don ganin ya rage kudin da ake kashewa wajen tafiyar da harkokin gwamnati. Saboda a wancan lokaci gwamnatin baya ba ta iya ko yin ayyukan ci gaba, wasu kananan hukumomi ma ba su iya biyan albashi ba tare da sun samu tallafin gwamnatin jihar ba.
Wannan dalili ya sa Gwamna El-Rufa’i ya dauki wasu matakai na tsuke bakin aljihun gwamnati saboda gwamnatin ta samu kudin yin wasu ayyuka ta hanyar daukar wasu matakai da suka hada da sadaukar da rabin albashinsa shi da mataimakinsa na wancan lokacin wato Akitek Barnabas Bala Banted. Sannan gwamnatin ta fito da tsarin asusun ajiya na bai-daya (TSA) inda ake tattara duk kudaden gwamnati zuwa asusun ajiya guda daya, inda a ranar 31 ga watan Agustan 2015 gwamnatin ta samu nasarar gano Naira biliyan 24 da suke boye a wasu asusun ajiye daban-daban na gwamnati da ba a san da zamansu ba. Haka kuma gwamnatin ta rage yawan kwamishioni daga 19 zuwa 14, sannan ta rage yawan masu mukaman siyasa.
A bangaren daukar nauyin manyan mutane da ’yan siyasa da gwamnati ke yi zuwa aikin Hajji da Jerusalam, Gwamna El-Rufa’i ya samu nasarar kubutar da Naira miliyan 221 da gwamnati ke kashewa duk shekara wajen kai ’yan uwa da abokan arziki aikin Hajji da Jerusalam.
Haka kuma, Gwamna El-Rufa’i ya dauki matakin tantance ma’aikatan jihar ta hanyar kimiyyar zamani (biometric berification) inda aka samu nasarar ceto Naira miliyan 120 da ke tafiya aljifan wadansu duk wata da sunan biyan albashi, alhali babu ma’aikatan illa na bogi.
Sannan gwamnatin ta yi kokari wurin toshe wata hanyar da kudaden talakawa ke zurarewa da sunan tallafin taki, ta fito da wani tsari wanda ta gayyato kamfanonin takin zuwa cikin Jihar Kaduna ta cire musu haraji, hakan ya saukar da farashin takin zuwa Naira dubu biyar kowane buhu.
Wani matakin da Gwamna El-Rufa’i ya dauka, shi ne ta fannin kudaden shiga inda aka samu karin kudaden shiga ta hanyar toshe duk wasu kafafen da kudaden haraji ko na shiga da aka amsa suke zurarewa zuwa aljifan wadansu, ba tare da gwamnati ta kara wa jama’a kudin harajin ba, kuma aka mayar da biyan kudin haraji zuwa bankuna da kuma amfani da na’urar P.O.S.
Wani babban matakin da gwamnatin Malam Nasir El-Rufa’i ta dauka domin samun kudin da za ta rika gudanar da manyan ayyuka musamman a kananan hukumomi shi ne na rage ma’aikata masu zaman kashe wando a kananan hukumomin. A baya akwai kananan hukumomin da suke da ma’aikata masu zaman banza ba su da abin yi sai dai karshen wata kawai su karbi albashi. A wasu kananan hukumomin ma an samu direbobi shida da suke tuka mota daya. A Karamar Hukumar Zariya an samu ma’aikata sama da 300 suna aiki a Sashin Gudanar da Mulki. Wannan yawan ma’aikata ya sa kananan hukumomi da dama ba su iya biyan albashi ba tare da gwamnatin jiha ta tallafa musu ba, balle har su samu rarar kudin da za su yi ayyuka. Kuma Gwamna El-Rufa’i ya dauki matakin kayyade adadin ma’aikata da kowace karamar hukuma ya kamata ta ajiye wanda wannan mataki ya haifar da da mai ido saboda dukkan kananan hukumomin jihar 23 suna iya biyan albashi har su samu rarar kudin gudanar da ayyuka a yanzu.
Bugu da kari, wani mataki kuma da Gwamna El-Rufa’i ya dauka shi ne na rage yawan masarautu zuwa tsohon tsarin masarautu kafin shekarar 2001, inda aka rage yawan gundumomi daga 390 zuwa 77, sannan yawan dagatai daga 5,882 zuwa 1,429. Wanda a baya duk nauyin wadannan hakimai da dagatai na albashinsu da sauran hidimominsu yana wuyan kananan hukumomi ne.
In kuwa aka dawo ta bangaren ilimi, Gwamna El-Rufa’i ya zo ya tarar da mutane da dama sun shiga harabar makarantu sun yi gidaje da shaguna. Akwai wanda aka samu ma ya gina gida kusa da dakin kwanan dalibai har ya hada bututun bayinsa da ramin sokawe na makarantar. Kuma ya nemi hukumar makarantar ta hana dalibai bude tagogin dakunansu saboda wai suna leka masa gida. Wannan zalunci na daya daga cikin abubuwan da Gwamna El-Rufa’i ya rusa, inda ya kwato wa makarantu da dama filayensu ta hanyar rushe duk wasu gine-gine da aka yi a cikin makarantun.
Misali shi ne na Kwalejin Alhudahuda da ke Zariya da Kwalejin Rimi College da ke Kaduna da sauransu. Sannan bayan kwato filayen makarantu daga hannun mutane, Gwamna El-Rufa’i ya gyara sama da makarantun firamare 400, kuma an gina sababbin ajujuwan karatu bene guda ashirin hudu a makarantu daban- daban da suke da cinkoson dalibai. An gyara makarantun sakandare da dama, an sanya kayan karatu da kujeru sama da dubu ashirin.
A bangaren aikin hanyoyi, gwamnatin tun a zango na farko ta kaddamar da wani shiri na gudanar da aikin hanyoyi na kilomita goma a kowace karamar hukuma, wasu kananan hukumomin fiye ma da haka, kuma wannan aiki an kammala a wasu kananan hukumomin wasu kuma aikin ya yi nisa. A wasu kananan hukumomin sai da aka biya diyya aka rushe gidaje da shaguna sannan aka yi titunan. An yi irin wadannan rushe-rushen bayan biyan diyya a kananan hukumomin Kachiya da Ikara da Zariya da Kaduna ta Arewa da sauransu. Haka kuma a inda ake bukatar fadada tituna an biya diyya kafin rushe gine-ginen don fadada titunan- an yi haka a Rigasa da Unguwar Dosa da Kawo da sauran wurare a cikin garin Kaduna da kewaye.
A takaice dai ana iya cewa a cikin shekara biyar da Gwamna El-Rufa’i ya yi yana mulkin Jihar Kaduna, ya rushe zalunci, ya gina adalci, sannan ya rushe duk wasu abubuwan da suka jima suna yi wa gwamnatocin baya tarnaki wurin kawo ci gaba. Don haka Gwamna Nasir El-Rufa’i, zalunci yake rusawa yana gina adalci. Saboda haka wadanda suka sanya masa sunan mai rusau, ko su yanzu sun ga irin alfanun rusau din da yake yi, da dama yanzu suna dawo suna cewa ‘SAI MAI RUSAU’ domin su yarda zalunce yake rusawa yana gina adalci, wanda abin da ake nema ke nan daga shugaban nagari.
Abdallah Yunus Abdallah