✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai mata 4 ya yi wa agolarsa kuma ’yar kanensa ciki

Wata yarinyar mai shekara 15, ta zargi mijin yayar mahaifiyarta mai suna Musa Haruna da ke zaune a garin Madallah a Jihar Neja kuma yake…

Wata yarinyar mai shekara 15, ta zargi mijin yayar mahaifiyarta mai suna Musa Haruna da ke zaune a garin Madallah a Jihar Neja kuma yake da matan aure hudu cewa shi ya yi mata cikin da daga baya ta haife.

Mahaifiyar yarinyar ta bayyana wa Aminiya cewa yarinyar ta gaya musu cewa mijin yayar mahaifiyarta mai suna Malam Musa Haruna wanda ke sana’ar wanzanci da gadi ne ya yi wa ’yarta wadda kuma ’yar kanensa ne ciki ne a lokacin da take gidansa, bayan matarsa wadda ke matsayin yayarta ta dauko ta daga wajensu shekara daya da watanni.

A zantawarta da Aminiya, yarinyar wadda aka sakaya sunanta, ta ce hulda a tsakaninta da wanda ake zargi ta fara ne a wani lokaci da ya bukaci ta bi shi zuwa gona da sunan taya shi aiki. “Ya ce zan taimaka masa dibar ruwa shi kuma ya rika yin fishi. Ni ban san shi da wata gona ba, kuma ban so tafiyar ba amma haka ya tursasa min tare da matarsa da nake wajenta, sai na bi shi kuma muna isa wajen wanda daji ne sai ya tursamini ya yi lalata da ni.Ya ce idan na kuskura na gaya wa wani sai ya kashe ni,” inji ta.

Ta ce: “Bayan nan kuma ya sake yi mini fyade kamar 3na watan azumin da ya gabata, yana kuma ba ni wani magani ya ce in sha da ke sauya min yanayin jiki. Yana yi min haka ne a lokacin da matansa hudu su ka tafi wajen karatun tafsiri da safe a lokacin watan Ramadan.”

Mahaifiyar yarinyar wadda ta taso daga kauyen Ligyara da ke kusa da Gadar-Gayan a Jihar Kaduna inda take aure. Ta ce ita kanta a gidan mutumin ta taso kasancewar an ba da ita raino ga yayar tata tun tana karama. “Shi ne ya jagoranci hada auren zumunci a tsakanina da kanensa, mahaifin wannan yarinyar. “Matar tasa da ke matsayin yayata ta dauko yarinyar ne bayan kai mana ziyara a wani lokaci. Ban so zamanta a gidan ba saboda sanin halinsa da na matarsa kuma duk kokarin da na yi don raba ta da gidan bai yi nasara ba, inda ya yi kememe shi da matarsa wadda take dora mata tallar gyada. Yarinyar ta gaya min cewa takan tura ta wajen mijinta da dare ta bi shi inda yake gadi bayan ta hada ta da wani abu da sunan ta kai masa, inji ta.

Yarinyar ta shaida wa Aminiya cewa wanda ake zargin yana yi mata fyade a wani kango da ke kusa da inda yake aikin gadi duk lokacin da aka aike ta wajensa. Ta ce matarsa ke tursasa mata lallai sai ta je wajen idan ta yi yunkurin bijire mata a kan hakan.

Mahaifiyar yarinyar ta ce ta gano ’yarta na dauke da ciki ne a lokcin da ta nemi ta zo kauyensu na Ligyara ta zauna da su ta koyi yi aikin gyaran shinkafa da suke yi.

“Na ga wata guda ta wuce ba tare da ta yi al’ada ba.A nan ne na tuhume ta, amma sai ta ce tana ganin al’adarta. Haka wata da muke tare a gidan ta nuna kokwanto bayan kula da yanayinta, inda ta karfafa min gwiwa cewa lallai a yi bincike a kai, hakan ya sa na dauko ta muka dawo nan Madalla aka je asibiti aka yi bincike, a nan aka gano tana dauke da cikin wata 7. Na sa ta a gaba a kan sai ta gaya min yadda ta samu cikin amma ta ki sai da na hada ta da wata malamar jinya da ke makwabtaka da mu da na kula ta shaku da ita. Ita ce ta yarda ta sanar da ita cewa shi ne ya yi mata cikin,” inji ta.

Ta ce da farko an kai ta wani gida ta haihu saboda gudun tsangwama a unguwar amma bayan ’yan kwanaki sai wadanda take wajensu su ka dawo da ita gidan da take.

“Sun sake kai ta wani gida a can ne ta haihu a gaban wata malamar jinya a makon jiya, bayan nan ne sai mutanen gida suka dawo da ita gidanmu, alhali ba su da labarin halin da ake ciki kuma bayan jin bayanin ne, suka dauki maganar suka kai gaban Masarautar Zuba da unguwarmu ke karkashinta, inji ta.

Aminiya ta samu labarin cewa da farko’yan bangan garin Zuba sun gayyato mutumin inda ya amince da cewa ya aikata lalata da yarinyar sannan aka dauki hotosa a bidiyo lokacin da yake bayanin wanda Aminiya ta gani.

Sarkin Fadan Zuba Alhaji Murtala Muhammad wanda ya jagoranci zaman, ya shaida wa Aminiya cewa daga bisani sun mika lamarin ga ofishin ’yan banga na garin Madalla saboda a can ne lamarin ya faru.

Kwamandan ’Yan banga na garin Madalla Alhaji Idris Salihu, ya ce shi ya ce a kai yarinyar asibiti inda aka yi mata karin ruwa kuma suka rike mutumin a ofishinsu. Ya ce sai dai ana cikin haka ne sai labari ya zo gare shi cewa wadansu kannen wanda ake zargi sun je asibiti sun auka wa mahaifin yarinyar, kan zargin an yi wa dan uwansu sharri.

“Da aka gayyato su nan, na bukaci wanasu ya mayar da bayani a gabansu, kuma a gabansu ya furta cewa lallai ya aikata haka, sai suka ja baya suka kama kuka,” inji shi.

Ya ce an rubuta yarjejeniya a tsakanin wanda ake zargin da ofishinsu, kan zai biya dukkan kudin dawainiyar da aka yi a kan yarinyar kama daga gwaje-gwaje zuwa haihuwa da aka kiyasta an kashe Naira dubu 49.

Ya ce ofishin ya tilasta masa da ya rika biyanta Naira dubu biyar duk wata a matsayin dawainiyar kula da jaririyar har zuwa yaye ta, kuma ya biya kudin hayar dakin da za ta yi zaman, sai kuma daukar dawainiyar jinyar jaririyar a duk lokacin da ta kamu da wani rashin lafiya.

Lokacin da wakilinmu ya je gidan wanda ake zargin a ranar Litinin don jin ta bakinsa an shaida masa ba ya nan. Kuma da ya nemi shi ta waya ya ce ya yi tafiya zuwa Jihar Katsina don neman kudin da aka ce ya biya, da ya ce sun kai Naira dubu 60. Kuma ya tabbatar da cewa an dora masa biyan Naira dubu biyar duk wata don kula da jaririyar.