Wata jami’a a kasar Togo ta karrama fitaccen mai shirya fina-finai na masana’antar Kannywood, Abdulrahman Muhammad wanda aka fi sani da Abdul Amat Mai Kwashewa da digirin girmamawa.
Jami’ar mai suna IHIRIS ta ba Furodusan digirin-digirgir na Dokta a fannin Sha’anin Mulki da kuma Gudanarwa.
- Shirin fim ya fi min siyasa – Mai Kwashewa
- 2023: Abin da ya sa YBN ta kaddamar da sabbin rassa 3 – Mai Kwashewa
An ba matashin digirin ne a wani kwarya-kwaryar biki a harabar jami’ar da ke Togo a cikin jerin bukukuwan yaye dalibanta a karshen makon nan.
A hirar da Aminiya ta yi da Nura Shariff, daya daga cikin na hannun daman Abdul din, ya ce jami’ar ta ba shi digirin girmamawar ne sakamakon wani zuzzurfan bincike da kuma bibiyar ayyukansa na taimakon matasa.
Sannan bayan dogon nazari, sai ta ga ya cancanta ta karrama shi da digirin domin ya zama abin misali da kuma koyi ga ’yan baya.
Matashin dan siyasan ya yi fice a wajen taimakon jama’a musamman ’yan Kannywood da jikinsa da kuma aljihunsa.
Shi ya kafa kungiyar YBN don tallata takarar Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ta shugaban kasa, a yanzu kuma shi ne Babban Darktan yakin neman zaben Tinubu a bangaren fadakarwa da nishadantarwa.