Wata mai jego dauke da jaririyarta mai wata biyar da haihuwa na zanga-zanga a ofishin gwamna kan rashin biyan albashi na wata 26.
Mai jegon ta ce tsananin halin da ta shiga a tsawon lokaicin da ba a biyan su albashin ya sa ba ta da zabi face ta fito ta bayyana halin da abin da ta haifa ke ciki.
- Mahara sun bindige mutum 40 a Nijar
- Rashin tsaftataccen ruwa: ’Yan Najeriya miliyan 60 na iya kamuwa da cututtuka
- Gobara ta tashi a Babbar Kasuwar Katsina
“Ina cikin tashin hankali har ta kai ga ba yadda na iya sai dole in fito da jarirayar tawa a cikin sanyi ga kwari na ta cizon ta,” inji mai jego Rita Ititim wadda kuma babbar alkali ce.
Alkali Rita Ititim ta bi sahun abokan aikinta da suka tare ofishin Gwamna Benedict Ayade na Jihar Kuros Riba, saboda shafe shakara biyu da wata biyu ba tare an biya su albashi ba.
Ta ce rashin biyan albashin ya jefa jaririyar cikin barazana iri-iri, kasancewar ba ta iya saya mata abinci, magani da sauran bukatu, ga shi kuma ana bin ta bashin kudin magani.
Ititim na daga cikin alkalai 29 na kotun Majistare a Jihar Kuros Riba da suka yi dafifi dauke da kwalaye suna bukatar gwamnan ya biya su hakkokinsu.
Mai magana da yawun alkalan, Solomon Abuo, ya ce, “A zaman da muka yi da gwamnan a watan Janairu tare da mataimakinsa da Kwamishinan Shari’an Jihar, ya yi alkawarin biyan mu bashin albashin da muke bi.
“Muna mamakin yadda har yanzu ya ki cika alkawarin da ya dauka.
“Abin takaici da kuma rashin tausayi da zalunci ne a ce gwamnati tana yi mana hakan; Wasunmu an tashe daga gidan haya saboda sun kasa biya.
“A zamanmu da shi (gwamnan) ne ya nada mataimakinsa, Farfesa Ivara Esu, ya jagorancin kwamitin kuma tuni ya mika rahotonsa.
“Abin da kawai ya rage shi ne ya sa hannu biya mu, amma ba mu san me ya hana shi ba,” inji shi.
Tun da farko da take bayani, babbar mai ba gwamnan shawara, Christian Ita, ta ce ba a bi ka’ida ba wurin daukar alkalan na Kotun Majistaren aiki.