A ranar Lahadin da ta wuce ne kulob din balencia da ke Sifen ya tabbatar da mutuwar daya daga cikin masu goya wa kulob din baya a lokacin da yake murna jim kadan bayan balencia ta rama kwallon da FC Barcelona ta jefa a ragarta. Tun a minti na 59 ne dan kwallon Barcelona Luis Suarez ya jefa kwallo a ragar balencia a gasar rukunin La-Liga na Sifen.
Sai dai a daidai minti na 86 wato ana saura minti hudu a tashi wasan ne sai dan kwallon balencia Santiago Mina Lorenzo ya rama cin da aka yi musu. A nan filin wasan ya barke da murna ciki har da marigayin. An ce ana cikin murna ne sai aka ga marigayin ya yanke jiki ya fadi kuma aka garzaya da shi asibiti kafin ka ce kwabo rai ya yi halinsa.
Tuni kulob din na balencia ya fitar da sanarwar mutuwar magoyin bayan nasa, inda ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin.
…Mai goyon bayan balencia ya mutu a lokacin da yake murna
A ranar Lahadin da ta wuce ne kulob din balencia da ke Sifen ya tabbatar da mutuwar daya daga cikin masu goya wa kulob din…